Idan ba a tabbatar da shi ba a matsayin sabon Sarki ba zai zama akwai shaku na cancantarsa a matsayin sabon Sarkin Zazzau.
Waɗanda suka ki bin dokokin Zaɓen Sabon Sarki. Don haka ita Gwamnatin Jahar Kaduna ta kai babban ɗan majalisar Sarki kara a kotu wato Wazirin Zazzau Alhaji Ibrahim Aminu kan ana zarginsa.kan wasu laifufuka.
Kutu tana gayyatarsa ne a kan zarginsa na buga hatimin bogi da kuma takardun mallaka na ƙarya da ya saɓa doka na sirri a hukumance. Ana buƙatar Waziri da ya bayyana a gaban Kutun Majistiri ta ɗaya (1) a Kaduna, Ran 15 ga watan biyu 2021.
Kotu tana ganin shi Waziri Zazzau a matsayin wanda ya fi kowa matsayi a masarauta, a dalilin rashin Sarki. Waziri shi ke da wuƙa da nama a masarauta. Shi ke da daman hurɗa da Gwamnati, haka nan ya shugabanci gudanar da zaɓe a masarauta. Ya yi aiki sosai wajen gudanar da zaɓe a Ranar 24 ga Watan Satumba 2020.
Waziri shi ne babban Ɗan majalisa a fadar Sarki wanda hakan ya ba shi daman hurɗa da Gwamnati a kan abin da ya shafi Masarauta.
Takardan da ta fito daga ofishin Kwamishinan ƙananan Huƙumomi zuwa ga masu naɗa Sarki domin shirye-shiryen yadda za a yi zaɓen bata ambaci wani sashin doka a hukumance da zai yi jagoranci abin ba, ma'ana kowane daga cikin ƴan takara zai iya neman da a ba shi yadda zaɓen Sarkin zai gudana, kuma babu wata sheda da ke nuna shi ne ya yi amfani da damar da yake da ita wajen bayyana wanda aka sahalewa ya fitar da takardar.
Ana nan kuma kwatsam yai wata irin rasuwa da ta sanya zarge-zarge, dukkanin masu naɗa sarki su biyar (5) kuma waɗanda da su ne aka gudanar da zaɓen sun sanya hannu a takardan zaɓen da aka yi.Sannan sun aike wa Kotu kofi na takardan da suka sanyawa hannu a lokacin da kotu ta gayyace su na su bayyana a gabanta Ranar 18 ga watan Nuwamba, 2020.
Matuƙar wani abu ya faru da Waziri to sarki da shi da Gwamna su ne waɗanda za a ɗorawa alhakin.
Wata kila ya zama shi ne na biyu a wanda zai rasu a nan gaba.
To mai ya sa ake zargin Waziri banda sauran masu naɗa Sarki, hakan na faruwa ne saboda shi Gwamna ba zai iya juya Waziri yadda yake so ba. Mutum ne da aka san shi da riƙon gaskiya.
A bangaren sabon sarki kuwa batun tabbatar da kujerarsa zai zama mai alamar tambaya? koda kuwa zai kasance, saboda haka zai kasance ya rage wa ita kotun majistiri na ta ko zata kai Waziri gidan yari na tuhume- tuhumen da take yi masa na aikata manyan laifuka.
Ana zargin kila shi ne mutum na biyu da zai rasa ransa a game da batun naɗa sarkin na Zazzau.
Abin tambaya a nan shi ne ko mutum nawa ne za su rasa rayukansu nan gaba game da batun Sarkin na Zazzau! A matsayin mu na ƴan adam mun yi imani da Allah da kuma aikata alkhairi dole mu tsare hakan. dole ne mu nemi kariya daga aikin sheɗan. Allah ya taimake mu.
Comments