top of page

Wanka da ruwan dan wake : katobarar El-Rufai wajen nadin sabon Sarkin Zazzau - Dr Nasir Aminu

Updated: Nov 18, 2020

Masu iya magana su na cewa duk yadda aka yi da jaki, sai ya ci kara.

Gwamna Nasir El-Rufai a cikin wani irin yanayi, ya zabi Ambasada Ahmad Bamalli, ya kuma naɗa shi sabon sarkin Zazzau. Rashin bin ƙa’ida wajen zaɓen sabon sarkin ya haddasa shiga kotu da gwamnati. Da wannan, gwamnan ya kuma yi nasarar gwara kan gidajen sarautar Zazzau.


Tun tale-tale, El-Rufai shugaba ne mai kawo rabuwar kai, wannan na cikin dalilan da ya sa ƙungiyar Lauyoyi ta NBA ta soke goron gayyatar da ta aika masa na yin magana wajen babban taronsu na shekarar 2020.


A jawabinsa wajen naɗin sabon sarki, El-Rufai ya yi iƙirarin shi ne shugaban farar hula na farko da ya samu damar naɗa sarkin Zazzau. Kamar wani Fir’aunan zamanin yau, sai ya yi barazanar sa ƙafar wando ɗaya da duk waɗanda su ka ƙi yin mubaya’a ga sabon sarkin. Mulkin farar hula tsari ne da babu wani shugaba tilo da ya ke da wuƙa da nama a hannunsa wajen jagoranci, hakan na nufin dole kowane mai rike da kujera ya bi doka. Sai dai kash, El-Rufai ya yi kunnen-ƙashi, bai bi doka wajen nada sabon Sarkin Zazzau ba.


Gazawar El-Rufai wajen aiki da doka ya jawo ya yi ta karance-karancen littatafai rututu, ya buƙaci lokaci barkatai domin samun fashin baƙin dokokin ƙasa daga masana da-dama.


Shari’ar da aka kai gaban kotu ta na ƙalubalantar saɓa wa sashe na 3 (1) na dokar naɗi da tunɓuke sarakuna na jihar Kaduna, wada ta ce: ‘Bayan mutuwar duk wani mai mulki…Gwamna ya na iya naɗa magajin (mai rasuwan) daga cikin jeringiyar waɗanda masu hurumin zaƙulo sarki kamar yadda doka ta tanada. Su ka fito da shi’


Bari mu yi gwari-gwari, doka ta ba gwamna damar naɗa wanda masu zaɓen sarki su ka fito da shi ne kawai a matsayin sabon sarki, ba wanda gwamnan ya ke so ba. Saboda haka, saɓa doka da yin ƙememe a aikata akasin hakan, raina aikin masu zaɓen sarki ne, wanda hakan ya na kai wa ga fatali da darajar sarautar gargajiya da mu ke matuƙar girmama wa. Idan masu zaɓen sarki ba za su iya zaƙuko wanda zai yi mai mulki ba, ina bada shawarar masarauta ta canza sunan aikinsu. Zaɓen wanda zai zama sarki aiki ne mai daraja, watsi da wannan tsari cin mutunci ne ga sarautar gargajiya.


A jawabin na sa, gwamnan ya bayyana cewa Ubangiji ne ya ba shi ikon gyara rashin adalcin da aka yi wa gidan sarautar Mallawa na cewa Turawan mulkin mallaka sun tsige Sarki Alu Dan-Sidi (1903-1920) daga karagar mulki ne a lokacinsa saboda saba wa dokar ƙasa, wanda su ka haɗa da cinikin bayi. Ga gwamnan, haramtacciyar naɗin da ya yi wa ɗanuwansa, duk ya gyara kura-kuren da aka yi, sannan ya wanke turawan mulkin mallaka da soso da sabulu tsaf. A wurina, babu abin da ya fi wannan danyen aikin fito da son-kan da El-Rufai ya ke da’awar adawa da ita.


Idan za mu soma gyara rashin adalcin da aka yi wajen tunɓuke sarakuna, sai El-Rufai ya fara gyara wasu kura-kuren da aka yi a baya. Turawan mulkin mallaka sun tsige Sarki Kwasau (1897-1903) daga gidan Bare-bari inda su ka kuwa naɗa Alu Dan-Sidi a kan kujerarsa. Haka zalika Sarkin Musulmi ya tsige Sarki Sambo na gidan Katsinawa ba tare da ya yi laifin fari ko na baƙi ba.


Har wa yau, gwamnan ya nemi a tausaya gidan Mallawa, ganin sun shafe shekaru kusan 100 ba su hau kan kujerar mulki ba. Idan gwamnan da gaske ya ke yi, sai ya tausaya wa gidan Sulluɓawa wanda rabonsu da sarauta fiye da shekara 160 kenan. Sarkin da ya taɓa fito wa daga gidan Sulluɓawa shi ne Abdulsalami (1860-1863), wanda ya mutu a kan karaga, ba tsige sa aka yi ba. Ina kuma sha’awar gaanin yadda zai gyara rashin adalcin da aka yi wa sarakunan Habe da su ka rasa mulki tun da sarakunan Fulani su ka shigo kasar a 1804.


Idan har da gaske gwamnan ya karanta littatafan nan (misali, Smith 1960) da ya ke cewa ya karanta, zai fahimci gidan Katsinawa sun shafe shekaru 73 ba su hau kan karagar mulki ba. A wannan lokaci, an yi sarakuna shida, biyar sun fito ne daga gidan Bare-bari. Asali ma a 1937, duka waɗanda su ka nemi mulki daga gidan Bare-bari su ke. Babu lokacin da sauran gidajen sarautan su ka yi yunƙurin ƙaurace wa doka ko gigin su soki tsarin ko ta wani irin hanya.


A jawabinsa, El-Rufai ya ce ya na so ya dawo da dokokin da ake bi wajen zaɓen sarakuna a daular Usmaniyya. Ya sani cewa mutanen nan masu daraja da ke da alhakin zaɓen sarki ba su taɓa wasa da dokokin ba. Ya na iya neman kare abin da ya yi, amma wannan ba zai canza gaskiyar abin da ya yi a gaban Ubangiji da kuliya ba.


Gwamnan ya ce zaɓin da aka yi, yin Allah ne, kuma ya buƙaci goyon bayan kowa a wajen sabon Sarkin. Al-Qur’ani ya ce: “Ka da ku kusanci marasa adalci, idan ba haka ba, wuta za ta ƙonaku.” Naɗin wannan sarki da aka yi rashin adalci ne, ina magana ne da yawun Sarakan Zazzau waɗanda su ka ƙi halartar bikin rantsar da Sarkin domin nuna rashin goyon bayansu, da kuma duk sauran ‘Yan Najeriya da ba su goyon bayan rashin adalci. Burin kowane ‘Dan Sarki a Zazzau ne ya ga cewa ba a ci mutuncin gidan sarauta ba. Ina sa ran El-Rufai ya yi na’am da zabin da kotu za ta yi nan gaba shi ma a matsayin zaɓin Allah.


Abin da ya dace shi ne a tafi kotu a ƙalubalanci wannan ƙarfa-ƙarfan zalunci na ƙaƙaba Sarki, domin a gyara kuren da gwamnan da jama’a su ka zaɓa ya yi. Hakan, hidimta wa masarautar Zazzau ne da kare gidan sarauta. Sabon sarki ba zai samu goyon bayan mutanen Zazzau ba, duk da barazanar da gwamnan ya ke ta faman yi. Mutane a shirye su ke, su nuna ƙarfinsu ta hanyar nuna adawa ga daniyya.


Ko da an bada sanarwar Ambasada Bamalli ya zama sabon Sarkin Zazzau, har ya amince da zaɓin, kuma gwamna ya naɗa shi, sai dai shari’a ta na kotu, ana ƙarar yadda aka bi wajen cin ma wannan matsaya, inda ake sa ran a ji gwamna bai da ikon da zai yi katsalandan. Halartar babban Alƙalin jihar Kaduna wajen naɗin ya jawo ƙila-wa-ƙala a zukatan jama’a game da shari’ar da ake yi. Shin ko za ayi gaskiya da adalci a wannan ƙara?


A je a dawo, idan ba ayi adalci ba, ɗanyen aiki irin wannan ya na buƙatar majalisar dokoki ta tsoma baki, domin laifi ne da aka yi da ya cancanci a tunɓuke gwamna daga ofis. Ka da mu manta, a 2008, majalisar tarayya ta tabbatar da cewa El-Rufai bai dace ya riƙe kowace irin kujerar gwamnati ba. Abin mamakin shi ne yadda ya samu tikitin takarar gwamna a jam’iyyar APC duk da takunkumin.


Za a fara zaman somin taɓin shari’ar a ranar 18 ga watan Nuwamba. Allah Ya sa gaskiya ta yi halinta.


Dr. Nasir Aminu ya yi asalin wannan rubutu a jaridar Premium Times (a harshen Ingilishi
351 views0 comments

Comments


bottom of page