An aika wa Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Aminu, takardan dakatarwa daga Gwamnatin Jihar Kaduna. Takardan ta fito daga Ministry of Local Government, wanda Permanent Secretary, Musa Adamu, ya sa hannu a madadin Kwamishinan, Jafaru Sani.
Wazirin Zazzau dai shine shugaban masu zaɓen Sarki ne a Fadar Zazzau. Yana aiki da sauran masu zaɓen Sarki huɗu ne. Su ne: Limamin Gari - Alhaji Dalhatu Kasim, Limamin Kona - Muhammad Aliyu, Makama Ƙarami - Alhaji Muhammad Abbas, and Fagacin Zazzau - Alhaji Umar Muhammad.
In an tuna, Waziri ne yayi shugabancin zaɓen sabon Sarkin Zazzau. Waziri da Limamin Kona da Limamin Jumma’a suka zaɓi Iyan Zazzau ne, Fagaci kuwa ya zaɓi Yariman Zazzau ne, sai kuma Makama Ƙarami ya zaɓi Turakin Zazzau.
Amma Gwamna yayi watsi da zaɓen nasu. Sai ya baiwa Ambassada Bamalli. Yin haka ne ya sa Iyan Zazzau ya garzaya kotu, wanda za’a fara sauraren karan a ranan Jumma’a 11 December 2020 a Kaduna State High Court.
Masu zaɓen sarkin dai sun ɗauki nasu lauyan ne don su faɗi gaskiyan abin da ya faru a lokacin zaɓen. Amma sabon Sarkin na ta matsa musu da su ɗauki lauyan Gwamnati.
Rashin haka ne yasa aka basu takardan tambaya a ranan Jumma’a da ta gabata, 12 November 2020. Ana zargin shi ne yasa aka shiga kotun Dogarawa aka yi watsi da kayan mai Alƙalin a ƙarshen makon da ta gabata.
A yanzu dai mun ji ɗaya daga cikin masu zaɓen Sarki ya yarda ya ɗauki lauyan Gwamnati. Ba mu dai san mai zai biyo baya ba, amma masu zaɓen Sarki na baƙatar addu’a don Gwamnatin Kaduna na iya musu illa ta wurin taɓa lafiyar jikinsu ko ma su halaka su.
Allah ya ƙara mana imani, Ya kuma shige mana gaba.
Comments