Kowane ‘Dan Adam ya yi murna da zuwan wannan zamani — karni na 21 da ya kubutar da mutane daga bauta, daniyya da duk wasu nau’o’in zalunci da aka yi a da. Mu kuma gode wa tsarin farar hula da sauran bangarorin gwamnati da su ka takaita karfin daidaiku.
Yunkurin Gwamna Nasir El-Rufai na amfani da watanni 30 na karshen mulkinsa wajen sauya tsarin sarautar gargajiya a jihar Kaduna, abin tausayi. Don haka akwai bukatar a nemi taimakon shari’a da majalisa su sa baki a gwamnati. Ba za a fahimci tasirin sauye-sauyen da za ayi wa masarautar ba, sai bayan wannan gwamnati ta shude.
A wajen bikin nadin Sarkin Zazzau, gwamnan ya jaddada cewa ya na kokarin yi wa dokokin sarautar gargajiya garambawul. Kafin yanzu ya yi irin wannan bayani a lokacin da ya gabatar da kundin kasafin kudin shekarar 2021. Ban karanta abin da kundin ya kunsa ba, amma daga abin da gwamnan ya ke fada, ya ambaci bukatar shigo da tsarin kama-kama tsakanin gidajen sarauta, da sunan gyara ba-daidai din da aka yi ba.
A tarihi, masarautar Zazzau ba ta san tsarin kama-kama ba. Ana barin kofa a bude ne ga kowane Saraki ya nemi kujera a duk lokacin da Sarki ya rasu. Masu zaben Sarki su kan zakulo wanda su ke ganin ya dace, sai su nemi Sarkin Musulmi ya tofa masu albarka. A lokacin da Turawa su ka karbi gwamnati, a 1987, Turawan mulkin mallaka sun dai nemi tabarrukin Sultan bayan zabin majalisar masu zaben Sarki a lokacin da aka tunbuke Kwasau.
Kamar wata kasuwar baja-koli, an kasance ana gwagwarmayar gaske wajen neman sarautar Zazzau, wanda hakan ya sa ya ke wahala wani gida ya yi baba-kere a Zaazau. A dalilin haka ne Sarki Aminu (1959-1975) ya fito takara shi kadai tal daga gidan Katsinawa, kuma daukacin majalisar masu zaben Sarki su ka mara masa baya.
A 1846, Sarki Mamman Sani ya samu goyon bayan majalisar masu zaben Sarki, ya gaji ‘danuwansa, Sarki Hammada, da albarkar Sarkin Musulmi. A 1897, an zabi Sarki Kwasau ya maye gurbin mahaifinsa, Sarki Yero. Sarkin Musulmi bai so aka ada nada Kwasau a kan mulki ba, amma masu zaben Sarki su ka tsaya tsayin-daka wajen ganin wanda ya fi dace wa ya hau kan karagar mulki. Wannan ne ya yi sanadiyyar da gidan Katsinawa su ka shafe shekaru 73 ba su ji kanshin mulki ba, ba tare da sun yi kukan an yi masu rashin adalci ba.
A arewacin Najeriya, masarautu da-dama sun watsar da tsarin kama-kama, kuma babu maganar dawo da tsarin. Misali a kasar Kano, an daina fito da Sarki a tsakanin duka gidajen sarautar Dabo, an kyale gidan Abbas kadai su cigaba da mulki. Jikokin Sarki Suleimanu wanda ya fara karbar tuta daga hannun Shehu Danfodio sai dai su hau kujerar masu nada Sarki. A 2014, Nasir El-Rufai ya yi farin cikin zaman abokinsa, Muhammadu Sanusi II Sarki (tubabben Sarkin Kano), wanda shi ma ya fito ne daga Abbas. Haka zalika a Katsina, gidan da aka bar wa sarauta na Ummarun Dallaje, bai cikin wanda ya karbo tutar Danfodio.
Masana tarihi za su ce wadanda su ka karbo tutar jihadi sun hau kujerar malamai ne a maimakon sarakai, kusan irin abin da Danfodio ya yi, wanda bai karbi mukamin Sultan ba. A sakamakon haka wasu gidajen sarauta su ka rasa mulki. Malam Musa na gidan Mallawa ya cigaba da zamansa a malami har ya bar Duniya. Amma biyu daga cikin ‘ya ‘yansa sun dare kujerar Sarkin Zazzau. Asali ma, wannan Sarkin na yanzu ba daga tsatsonsu ya fito kai-tsaye ba, kamar yadda gwamna da shi karon kansa (Sarkin) ya ke kuskuren fada. Amma ba haufi Amb. Bamalli jinin Mallam Musa ne.
Shakka babu akwai masarautu kamar ta Lafia inda aka cigaba da aiki da tsarin karba-karba har gobe. Akwai kuma masarautun da ba a dade da yi wa irin wannan tsari kwaskwarima ba, misali kasar Bida. Amma dai babu kukan rashin adalci ko kiran a sauya dokokin.
A jawabinsa wajen nada sarki, El-Rufai ya yi da’awar cewa Ubangiji ya aiko shi domin ya gyara zaluncin da aka yi wa gidan Mallawa, domin Turawan mulkin mallaka sun yi rashin adalci wajen tunbuke Sarki Alu Dan-Sidi. Hujjoji sun tabbatar da cewa an an cire masa rawani ne saboda rashin gaskiya da cinikin bayi (duba litaffin M.G Smith, 1950). Za a iya jefa wannan zalunci a rukunin rashin gaskiya. Yin hakan ya na nufin duka sarakunan da gwamnoni su ka nada bayan shekarar 1920 ba na halal ba ne. Kenan, Amabasada Bamalli ne Sarkin gaskiya da aka nada a shekara 100.
Tun da ya na ikirarin Ubangiji ya aiko shi ya yi gyara, sai ya fara la’akari da gidan Sullubawa da su ka yi shekaru 160 babu mulki. Gidan Bare-bari da su ma sun yi shekaru 61 ba tare da mulki ba, amma ba su yi kukan rashin adalci ba. A wurina, shekaru 100 da Mallawa su ka yi babu mulki a hannunsu, nufin Ubangiji ne, ba zalunci kamar yadda Gwamnan ya ke nema ya nuna a jawabinsa ba. Haka kuma kaddarar Ubangiji ne da Marigayi Sarki Shehu Idris (1975-2020), ya yi mulki na shekaru 45, da su ka taru su ka bada shekaru 100 da ake magana. Nufin Ubangiji ba zai taba zama zalunci ba, kamar yadda zalunci ba zai taba zama nufin Ubangiji ba.
A karshe, kokarin gyara abin da aka yi kuskuren fahimta da rashin adalci, zai kai ne kawai ga wani sabon rashin adalcin. Ka da a canza salon zaben sarakuna a jihar Kaduna, a bambanta sa da sauran masarautu a arewacin Najeriya da yammain Afrika. Abin da ya dace a yi shi ne, a bar masarautun gargajiya a yadda su ke, yadda turawan mallaka da gwamnonin soja su ka gani, su ka kyale.
Dr. NasirAminu, malami a Jami’ar Cardiff Metropolitan ta Ingila, ya rubuta wannan da harshen Hausa a jaridar Daily Trust
Comentários