top of page

Barazana ta sa Alkalin da ke sauraron karar sarautar Zazzau tunanin hakura da shari’a

Updated: Oct 27, 2021

Alkalin babban kotu ya na kokwanton cigaba da sauraron shari’ar kujerar sarkin Zazzau a dalilin sha’anin tsaro.


Ana yi wa Alkali barazana da ransa, yayin da ‘yan sa-kai su ka kawo masa agaji a lokacin da ya ke tunanin raba kansa daga karar.


Alkalin babban kotun jihar Kaduna ya na duba yiwuwar zame wa daga shari’ar da aka kai gaban kuliya a kan nadin sarkin Zazzau.


Alkalin ya sa 11 ga watan Disamban 2020 a matsayin ranar da za a fara zaman somin-tabin shari’ar.

Amma a yanzu Alkalin ya na tunanin watsi da shari’ar daga teburinsa muddin ba za a maida hankali game tsaron ransa ba.


Alkalin ya nuna damu wa cewa ya ga wasu miyagun mutane a kan babur a ranar Alhamis su na bibiyarsa, abin har sai da ta kai ya nemi taimakon wucin-gadin ‘yan sa-kai a cikin dare.


A ranar Laraba, Alkalin ya bayyana cewa an shiga ofishinsa a babban kotun Dogarawa, an yi lalube a karshen makon makon da ya gabata. An yi ta’adi sosai, ana zargin wadanda ake kara ne su ka yi kokarin sauya takardu biyu da aka gabatar wa kotu. Na farko shi ne bayanin shaidun wanda masu zaben sarki su ka sa wa hannu, sai wata takardar kalubale da wadanda ake tuhuma su ka gabatar.


An kuma rahoto cewa gwamnatin jihar (Kaduna) ta na yi wa masu zaben sarki barazanar su canza lauyoyinsu, su zabi babban lauyan gwamnati domin su samu damar canza rantsuwar da su ka yi. Barazanar da gwamnatin jiha ta ke yi ce ta yi sanadiyyar takardar sammacin da aka aika a ranar 12 ga watan Nuwamba, 2020. Zuwa yanzu, daya daga cikin ‘yan majalisar masu zaben sarkin ya zabi babban lauyan gwamnati a matsayin wanda zai kare shi.


Sai dai a ranar Alhamis, 19 ga watan Nuwamba, 2020, gwamnatin jihar Kaduna ta dakatar da Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Aminu, bayan ya ki amince wa ya canza lauyansa

424 views0 comments

Recent Posts

See All
bottom of page