top of page

Yadda ta kaya a zaman tattaunawa na jin ƙarar bada sarautar Sarkin Zazzau a ranar 11 Disamba 2020.

Updated: Oct 29, 2021

Abu biyu ne suka faru, kuma ga yadda muka fahimce su, kamar haka


1. Fagachin Zazzau ya canza lauya. Ya kuma yi haka ne don son zuciyanci, kaman yadda shari'a ta yardan mishi. Dama shi lauyansa daban da sauran masu zaɓen Sarki. Masu zaɓen Sarki guda uku basu canza lauya da ke wakiltansu ba, amma lauyan gwamnati ke wakiltan Limamin Jumma'a.

An ɗaga sauraren ƙara sai 14 da 15 ga watan Janairu 2021. Kuma alƙali ya bada umurni a baiwa Fagaci takardan gayyata, ya rage mishi ya zo da kansa ko ya aiko lauyan da zai wakilce shi, wanda ana hasashen lauyan gwamnati ne


A zahiri, ba abin da zai canza ta wurin wani mai zaɓen Sarki ko da sun canza lauyoyi, saboda sun riga sun bada shaida a kotu tun-tuni.


2. Lauyoyin gwamnati basu kawo takardan jawabin kare kansu ba.

Alƙali, Kabir Dabo, bai jidaɗin haka ba, kuma ya faɗa musu hakan. Yayi ma lauyoyin gwamnati nasiha akan su daina wasa da sana'a. Kuma Aƙali ya tuna musu da cewa akwai dokan gama shari'an da gaggawa..


A fahimtarmu, in lauyoyin gwamnati basu kawo takardan jawabin kare kansu ba, lauyoyin mai ƙara na iya tambayan alƙali ya yanke hukunci bisa takardan ƙara da suka bayar. A hasashenmu, wanda ba hasashen ƙwararru bane, muna fatan za'a gama wannan shari'a zuwa ƙarshen watan biyu ta 2021. In Allah ya yarda.


346 views0 comments
bottom of page