top of page

Yunkurin yi wa masarautar Zazzau katsalandan zai jawo a kafa mummunan tarihi a Arewa –Dr. Nasir Amin

A halin yanzu mutanen Najeriya su na jiran zuwan ranar 29 ga watan Mayu, 2023 ne domin ganin karshen gwamnati mai-ci da ta kafa tarihin durkusar da tattalin arzikin kasa. ‘Yan Najeriya kuma har wa yau, suna sa ran a ranar 11 ga watan Disamba, 2020, a fara shari’ar Sarkin Zazzau da aka nada ba tare da an yi adalci ba.


Kungiyar lauyoyi na kasa, NBA ta zuba tabarau, ta zura idanu, tana kallon yunkurin da gwamnan (na jihar Kaduna) yake yi wajen fusata wannan shari’a. An auka wa babban kotun tarayyan da ake shari’ar, Alkalin ya nuna cewa rayuwarsa tana fuskantar baraza, ana tursasa masu zaben sarki su amince da babban lauyan gwamnati (kwamishinan shari’a) a matsayin wanda zai kare su a kotu, an kuma dakatar da guda daga cikinsu (masu zaben sarki).



An bar El-Rufai shi kadai yana ta faman kare danyen aikin da ba za a iya kare wa ba wanda shi kansa yake damunsa, kuma yake taba farin jininsa, a lokacin da ya ke harin inda zai shiga a tafiyar siyasarsa. Mutumin da ake yi wa kallon mai tsaya wa kare bin dokar kasa, ya na neman dawo da farin jininsa da ke zagwanye wa a wajen jama’a.


Ba tare da an yi mamaki ba, yunkurin da yayi, ya sake jefa gwamnan a cikin wani tsaka mai wuyan ne. A ‘yan watannin baya, jama’a za su iya tuna wa kar, lokacin da Lauyan wani shahararren mutumi suka kira tunbuke shi da aka yi daga karagar mulki a matsayin abin da ya saba doka, ya ci karo da tsarin mulki. Jama’an nan zasu iya tuna hirar da BBC tayi da wannan mutumi a Fubrairun 2014, inda yace zai kalubalanci dakatar war da shugaban kasa na wancan lokaci ya yi masa, domin yak are martabar ‘yancin babban bankin kasar. Kalaman da mai wannan jawabi ya yi game da sha’anin masarautar Zazzau ya nuna bai da daraja, bai da magana daya, kuma bai iya hakuri da halin da ya tsinci kansa.


Da ban mamaki ganin cewa duk da karambaninsa na fassara littatafan musulunci daga Larabci zuwa harshen Hausa, bai iya samun ko da wani layi daya da zai goyi bayan saba dokar da El-Rufai ya yi ba. Sai dai, yana ikirarin ganin damar Ubangiji ne ya sa gwamnan ya saba doka, ya nada Sarki, har ya na yin wasu barazana. Yin Ubangiji shi ne a bi doka, kuma Allah da muke bauta ba ya goyon masu zalunci.


A matsayinsa na wanda zai amfana kai-tsaye, wannan mutumi ya yi kasa-a-gwiwa da kokarin kare tsarin karba-karba wajen neman sarautar Zazzau. A 1963, mahaifinsa bai je ya yi wa sabon Sarkin Kano gaisuwa a lokacin da ya samu sarauta ba, saboda ya rasa takara. Wannan mutumi ba ya amanna da karba-karba ba, idan kuma ya ga abin yana goyon bayan ra’ayinsa, sai ya canza-sheka. Ina yake a lokacin da aka dakatar da tsarin karba-karba a masarautar Kano kusan shekaru 200 da suka wuce? A madadin haka, ya nemi mulki ne, ya shiga cikin masu neman takara, kuma ya samu nasara a wajen masu zaben Sarki. Ina yake da iya-maganarsa a lokacin da Katsina ta daina karba-karba fiye da shekaru 100 da suka wuce.


Hujjoji tamkar rana a lokacin sallar azahar sun tabbatar da cewa gidan Mundubawa da Dallazawaare da kakanninsu suka karbi tutar Kano da Katsina daga hannun Danfodio, sun yi shekaru 200 da 100 ba tare da sun yi mulki ba. Duk da haka jikokinsu, suna aikinsu a masarautunsu. Maganar ita ce, babu ruwan al’adun kasar Arewa da tsarin karba-karba.

Duk da karance-karancen wasu littatafai, gwamnan ya nuna bai fahimci tsarin shugabancida tafiyar masarauta mai tarin gidaje irin kasar Zazzau ba. Salon neman sarautar Zazzau bai taba zama karba-karba ba, kuma ba a taba ware wa wani gida na musamman kujerar mulki ba. Ya nemi ya nuna cewa yana kokarin ceto gidan sarautar da ke fuskantar barazana, a lokacin da yayi watsi da sauran wadanda aka manta da su kamar gidajen Habe da Sullubawa.


A kaddara gwamnan yayi nufin watsi da cancanta ne saboda zaluncin da aka yi wa Sarki Alu Dan Sidi. Meyasa ya yi watsi da jikan tsohon Sarkin da ya rage kadai a raye a Duniya, Alhaji Saidu Mailafiya, Ciroman Zazzau, wanda mahaifinsa Madaki Sa’idu shi ne babban ‘dan Sarki Alu Dan Sidi? Kamar yadda takardun zaben masu nada sarki da aka gabatar a gaban kotu, ya nuna, Alhaji Saidu Mailafiya ya zo na 8 ne cikin masu takarar, ya samu maki 57%, bai da tazara sosai da Sarkin da gwamnan ya zaba, wanda ya zo na 7 da maki 62%. Wannan zabi ya fallasa gazawar gwamnan na yin zabi tsakanin cancanta da gaskiya.


A gajeren wa’adinsa, wannan dambarwa ta sa ya maida masarauta abin wasan siyasa ga gwamnatin da za ta zo nan gaba, wanda ya sa aka maida tsige Sarki abin sauki da ba za a kalubalanta ba. El-Rufai ya kafa sabon tarihi da sauran gwamnoni za su nemi suyi koyi da wannan mummunan aiki idan ba a kalubalance shi ba. Abin da ake tunani an yi ya wuce, zai zauna na din-din-din.


Babban tasirin wannan aiki na El-Rufai ba zai bayyana ba sai can bayan ya bar gidan gwamnati. Allah ya tsaremu, idan aka dauki wannan aiki, zai jawo tashi-tashina daga mutanen sauran kasashen Arewa irinsu Kano, Katsina, Ilorin, Bida, Sokoto, Hadejiya da sauransu, su nemi a dawo yadda ake tafiya kafin 1804. Kaddara an dauki jawabin da gwamnan ya yi a gundarinsa, hakan zai yi sanadiyyar rushewar yadda abubuwa suke gudana, wanda wannan zai iya kai ga barkewar rikici a masarautun Arewacin Najeriya. Domin kuwa an tsara sarautar gargajiya ne domin su yi tasiri a cigaban tattalin arzikin kasar nan, tasirin wannan aiki zai zama tabarbarewar cigaban tattalin arziki. Zai kuma iya haddasa barazanar rashin tsaro a yankin Arewa da yake tafarfasa ko a yanzu.


63 views0 comments
bottom of page