Tun shekarar 1804, kujerar sarauta ta kasance k’ashin-bayan tsarin shugabanci a Daulolin Fulani a kasashen Arewacin Najeriya. Sarki ne yake rike da kujera mafi martaba, kuma yake kan karagar ta fi kowace karfi. A matsayinsa na shugaban addini, ana bukatar Sarki ya zama ya nuna abin da musulunci ya ce a wajen jagorancinsa.
Ana gadon sarauta ne ta dangin mahaifa (na wajen uba), an kaiyade neman kujerar ga ‘yan gidan sarauta. Tun daga kuruciya, ‘ya ‘yan sarakai su kan fara lakantar harkar shugabanci a fada, a daidai lokacin da suke samun ilmin boko kamar sauran ‘ya ‘ya. Bayan tsawon lokaci, su kan fara samun kafa da shiga a fada. Daga nan suke samun karbu wa da goyon baya a wajen manyan kusoshin gidan masarauta.
Wannan mubaya’a ce take tasiri ga ‘dan gidan sarauta wajen samun rawani ko ya rasa.
Kamar a duk tsarin damukaradiyya, babu wani gida da ake ware wa damar kamun kafa a fada. Samun mulki ya danganta ne da karfin ‘su-wa-da-wa ka sani’ da ittifikin wadanda ake yin ta da su da sauran manya a harkar. Don haka haihuwar mutum a gidan sarauta yana halatta masa samun mulki ne kawai, amma ko kusa ba wannan kadai yake sa shi ya zama ya hau karagar mulki ba.
A dalilin haka, kokarin Saraki na samun alaka da manya a ciki da wajen masarauta ne yake sa ya shiga cikin ‘yan gaba-gaban wadanda suka cancanci hawa kan gadon sarauta idan Sarki ya yi wafati.
Bayan rasuwar Sarki, masu zaben sabon sarki suna amfani da hanyoyinsu na gargajiya su zabi Magajinsa bisa al’adar Musulunci. Kafin Turawan mulkin mallaka su murkushe Daular Usmaniyya, Sarkin Musulmi ne yake da ikon amince wa da zabin da majalisar masu zaben Sarki suka yi. Daga baya aka maida wannan aiki ya rataya a kan gwamnan Turawan mallaka na Birtaniya da suke ganin sun fi kowa sanin yadda ya kamata ayi. Da aka samu ‘yancin-kai, wannan nauyi ya dawo ya rataya a kan Firimiyan Arewa, a karshe ya koma kan gwamnonin jihohi.
A tarihin sarautar Zazzau da mafi yawan masarautun Arewacin Najeriya, a kan wannan tsari ake tafiya, an cigaba da bin wannan al’adda illa a wasu tsirarrun lokuta masu ban-takaici. An samu wannan shan ban-bam ne a kasar Suleja a 1993, Sokoto a 1992, Gwandu a 2003, Borgu a 2000, Kano a 2016. A duk wadannan wurare, babu inda aka aka yi wa doka karon-tsaye kamar yadda aka yi a Zazzau a 2020.
Kafin yanzu, kasar da aka yi wa doka hawan kawarar hauka ita ce Borgu, inda aka yi watsi da matakin da masu zaben Sarki suka dauka saboda zabin gwamna. Amma abin da ya auku a Zazzau yanzu, ya zarce abin duk da ya wakana a Borgu.
A Sokoto, gwamnatin soji ta tunbuke Sarkin Musulmin da majalisa ta hadu ta zaba. Wannan shine lokacin da wasu daga waje su kayi wasa da sha’anin sarauta tun bayan tunbuke Sarki Sanusi I da aka yi daga Kano a shekarar 1963. An yi koyi da irin wannan aiki a Gwandu, inda aka yi ta fama da zuwa kotu bayan wannan katsalandan, kamar yadda ta faru a Kano.
Karshenta dai, tasirin abubuwan da suka wakana a wadannan masarautu shi ne mummunan rabuwar kai a kasashen, wanda hakan ya dakusar masu da cigaban tattalin arziki. A duk lokacin da aka tunbuke wani Sarki, ana rusa alakar dake tsakanin dangi, goyon-bayan siyasa ta kan canza alkibla, ana rasa yardar al’umma, duk da cewa a karshe za a zo a manta da wadanda suka yi wannan aika-aika.
Lamarin Zazzau ya sha ban-bam ta bangarori biyu. Na farko ta yadda gwamna ya ci mutuncin al’adar mutane wajen nadin Sarki. Akwai ban-tsoro game da yadda gwamnan yaci zarafin sarautar gargajiya. Gwamnan ya jefi masu zaben Sarkin da zargin bogin karbar cin hanci da rashawa. An kai wa mutane uku da suka fi muhimmanci a majalisar hari: Waziri, Limamin Kona da Limamin Juma’a. Wadannan mutane uku sune su ke rike da rawanin malanta a fada, suna da tasiri a cikin masarauta. Ta jifan wadannan gungu da zargi, gwamnan yana kokarin yaudarar jama’an gari, ya ruda su wajen yin abin da yake so. Gwamnan da yake mulki ta kafafen yada labarai, kamar shugaba Trump, shi ne yau yake kwakwazon a rika gudanar da abubuwa a cikin sirri.
Na biyu gwamnan yana yunkurin wulakanta shari’ar da ake yi domin kalubalantar matakin da ya dauka. Ana ji-ana gani gwamnan yana yi wa masu zaben Sarki barazana, wadanda suna cin gashin kan-su a karar da aka shigar, yana so su dauki wanda yake so a matsayin Lauyansu. An dakatar da daya daga cikin masu zaben Sarkin, an aika wa sauran takardar sammaci, har wani daga cikinsu yayi abin da gwamnan yake so. Haka zalika an shiga an fasa kotun da ake shari’ar, bayan Alkali ya ki kai karar zuwa inda Lauyan gwamnati yake so. Akwai kuma labarin ana yi wa Alkalin dake sauraron karar barazana.
Duk da haka dai, karar da aka kai gwamnan yana jawo rabuwar kai a masarauta. Ana sa ran cewa za a iya kalubalantar hukuma a duk lokacin da aka yi rashin adalci. Gwamna yana fahimtar cewa rusa turakar da take rike da sunan Afrika – dinbin tarihin da ake ji da shi, ba abu ne mai sauki kamar karatunsa a littafi ba.
El-Rufai sai ya yi da gaske, ya yi fada da dakaru da-dama, daga ciki har da Sarakan kasar Zazzau, face wasu tsirarrun malalata, akasari irin wadannan Sarakai ba su da komai wajen karfin takarar sarauta face cewa su ‘yan na-gada ne – suna da nasabar gidan sarauta.
Nasir Aminu babban malamin ilmin tattalin arziki ne a jami’ar Cardiff Metropolitan.
Comments