top of page

Kudirin Doka Na Masarautar Gargajiya-Shirin Rusa Yadda Tsarin Mulki KeTafiya

Updated: Oct 28, 2021

Hanya Mafi Sauki Na Rushe Dokar Da Ba Ta Dace Ba, Ita ce Tirsasa Aiwatar Da Ita - inji Abraham Lincoln



Ana kallon masarautar Zazzau a matsayin masarautar gargajiya da ta zama abin kwatance a Najeriya saboda irin tsare-tsaren da take da su masu kyau. Masarauta ce wadda a sakamakon tsarin da take da shi na amfani da salon jagoranci irin na gargajiya da al’adun Fulani ya sa ake gamsuwa da tsare-tsarenta. Masarautar na da tsarin aiwatar da abubuwa yadda ya kamata saboda irin yadda take da kusanci na al’umarta. Irin bayanan da ake isar wa da gwamnati game da zamantakewa da jin dadin al’uma shi ne ke tabbatar da cewa akwai tsare-tsare masu kyau.


A duk lokacin da aka sami wata baraka tsakanin shugabannin siyasa da al’umarsu, sarakunan gargajiya ne ke iyaka kokarinsu na shiga tsakani don ganin al’amura sun koma daidai.Wani kuma na iya yi musu kallon masu ci da siyasa ne kawai saboda irin yadda al’uma ta amince musu da kuma yadda tarihi ya nuna irin amincin da suke da shi da al’umar tun da can. Shiga su ga harkokin siyasa yana da fa’ida saboda kusancin nasu da al’uma. Su ne iyayen al’umar da za a iya tunkara da duk wani abu in ya taso saboda yadda aka dauke su tamkar ma ba jagorori ko sarakuna ba.An yi zango-zango na mulkin siyasa wato na farar hula har ma da na soji, amma duka sun gamsu cewa shuka gaskiya ga al’uma a mulki shi ne abin da ya fi dacewa.


Mahaifina ya rasa ransa a dalilin kalubalantar yadda aka bi aka nada sabon sarkin zazzau a kotu.Tun bayan rasuwarsa, El-Rufa’I ya yi ta yunkurin ganin an tabbatar da nadin da aka wa sarkin na yanzu.Akwai shaida na taka doka da sauya wurin aiki da soke sunayen mukamun sarauta da soke hakin mallakar filaye da rushe gidaje duk don ganin an yi shiru game da nadin sarkin.Sai dai yunkurin bai yi tasirin komai ba face ma fito da rashin iya mulkin sa da rashin hangen nesa da ma rashin sanin makaman shugabancin gaba daya - wannan shi ne babban misali na dan-wadan siyasa


Ganin cewa wa’adin El-Rufa’i bai wuce nan da shekaru biyu ba ya kare, hakika zai kare ne a tutar banza.Ya kudiri aniyar ganin ya zubar da martaban daya daga cikin tsofaffin masarautun kasar nan.Yana son ya zubar mata da kima da sunanta da ta dade da shi ta hanyar haddasa fitina da rashin aminci a cikin tsarin masarautar da kawar da gasar da ke tsakanin gidajen sarauta yadda hakan zai sa a rika samar da shugabanni masu rauni.


Shirin da ake shi ne na kudirin dokar masarauta a jihar Kaduna. An ma aike wa da majalisar dokokin jahar Kaduna har ma an yi mata karatun farko. Manufar kudirin shi ne na ba El-Rufa’i dama na cim ma burinsa na yin mulki irin yadda ya ga dama - A ‘yan watanni kawai da suka rage masa. Sarkin Zazzau ya yi maraba da kudirin, amma ya san ba za ta sa nadin nasa ya halatta ba.


Ba zan yi mamaki ba idan har aka ce za a sanya hannu ga kudirin ya zama doka har El-Rufa’i ya sa hannu daga nan zuwa wani dan lokaci, da kuma yadda sarkin ke zama me amincewa da lamarin. Amma ina da yakini kan cewa abin da sabuwar gwamanti za ta fara yi, shi ne na rushe kudirin dokar, ina kuma yi wa dukkanin su fatan tsawon rai da lokacin da za su ji kunyar abin da suka aikata.


Idan har kudirin ya cim ma nasara, hakan zai rushe dukkannin kyawawan tsare-tsaren da magabata suka yi a baya.Za ta rushe tsarin girmama manya da irin amincin da ke tsakanin masarauta da al’uma.


Kudirin kunshe yake da abubuwan da za su raunana tsarin masarauta.Kudirin ya bullo da tsarin karba-karba wanda ma ba zai yiwu a amince da shi ba, shi ne wai gidan sarautar Bare-bari su ne masu hawa kan gadon sarauta nan gaba.Sannan sai gidan Sullubawa su biyo bayansu. Dabarar kirkiro da karba-karbar shi ne domin a hana gogayya da gasa wajen neman sarautar wanda hakan zai kawar da martaban masarautar Zazzau.


Kudirin ya kuma kunshi batu na sanya matakai na masu zaben sarki wanda hakan bai daga cikin hurumin gwamnan. Kudirin ya kuma kunshi cewa, gwamna zai nada karin mutum hudu cikin masu zaben sarki. Bisa al’ada doka ba ta ba wa gwamna dama na nada karin mutum hudu cikin masu nada sarki ba ko da wani irin dalili kuwa. Sabon nadin da aka yi na masu zaben sarki domin cike gurbin Long Kwo bayan shekaru 33 zai taimaka wa wannan shirin. Hakika abin yana bukatar a lura da kyau, kuma ga shi muna tare da mutumin da yake da karancin sani in ban da kansa da ya sani.


Akwai shiri na nada limamin masallacin Sultan Bello a matsayin daya daga cikin masu zaben sarki a cikin kudirin dokar. Sarkin da aka zaba bisa ka’ida da cancanta ne kawai zai iya magana a kan irin wannan kwabar.Limaman masallacin Sultan Bello ‘yan Izala ne, ita kuma masarautar Zazzau an gina ta ne kan tafarkin Darika. Kamata ya yi a ce su kan su bangaren Izalar su nuna rashin goyan bayan hakan. Limamin masallacin Sultan Bello kusan ma za a iya cewa ba dan asalin kasar Zazzau ba ne, kuma ba shi da cikakken masaniya game yadda al’amuran masarautar ma suke tafiya. Don haka, babu wata gudunmuwa da zai ba shugabancin masarautar. In da a ce alheri aka kulla a kan wannan lamari, to ai da El-Rufa’i ya nemo wani daga cikin bangaren Izala cikin gidajen da suka gaji abin.Alal misali, limamin masarautar Zazzau fa sarkin Zazzau ne ke nada shi, shi kuwa limamin masallacin Sultan Bello sarkin musulmi ne ke nada shi.


In da a ce El-Rufa’i na da masaniya sosai game da tarihin masarautar Zazzau, zai fahimci dalilin da ya sa sarkin Zazzau Kwasau ya yanke hukuncin yanke alaka da Sakkwato a shekarar 1897. Sarki Kwasau ya kasance wanda ke jagoranci irin na hada kan al’uma bisa tafarkin da magabatan iyayenmu suka bari. A lokacin mulkin mahaifinsa a (1890-1897), sarki Kwasau ya dauki mataki na mallakan bindigogi da sauran makamai da kamfanin Royal Niger Company da ke Niger ke sarrafawa. A lokacin da mahaifinsa ya rasu, Kwasau ya nada kansa a matsin sarki a shekarar 1897 saboda da Wazirin Sarkin Musulmi ya so ya nada wani tsohon makahon dan Sarki ne, gashi kurma, a matsayin sarkin Zazzau. Kwasau ya dauki matakin da ya dauka ne ta la’akari da kuskuren tunanin da Fadar sarkin musulmi ta yi a wancan lokaci wanda ya yi hannun riga da na magabatan masarautar Zazzau.


Wannan mataki ya sanya Fulanin Zariya suka hada kai tare da mara wa Kwasau baya suka juya wa Sakkwato baya.A Shekarar 1901 ya gayyaci Captain (Lord) Lugard wajen kafa hukumar British Garrison a Zariya domin tabbatar da ganin cewa, kasar Zazzau ta zama mai cin gashin kanta a bangaren jagoranci. Tun a wancan lokaci, har yanzu kasar Zazzau ba ta taba zama karkashin fadar sarkin musulmi ba wato Sakkwato.


Har ila yau, kudirin dokar ya kunshi cewa, gwamna shi ne zai nada sarki bisa la’akari da amfani da ka’idojin da kwamishina ya bayar kan yadda za a yi nadin ba tare da bin tsarin yadda masu nada sarki ke yin zaben ba. Ta kunshi cewa su masu nada sarki, nasu kawai su tantance tare da mika rahoton wadanda suke neman sarautar. Domin dai a sami tsari na sauke sarki daga kan kujera cikin sauki tamakar sauke mataimaki, dokar ta ce gwamna na iya sauke sarki bisa yadda minister ya ga cancantar abin wato har idan ya gamsu cewa saukewar ita ce abin da ai’uma ke bukata.Wannan yana nuna cewa, ba ma za a yi la’akari da masu nada sarkin ba har in za a sauke shi. Ina ganin ma ya kamata a sauya wa masu nada sarkin suna domin kudirin dokar ya kwace dukkanin alhakin da ya rataya a wuyansu.


Har wayau, kudirin dokar ya kunshi cewa sarautar hakimta ba za ta kasance ta gado ba ce.Ana nufin ba a samun biyayya da gaskiya da aminci a wancan tsarin sarautar gargajiya da za a sami kyawawan dabi’u, sai dai ta hanyar gado. Irin wannan bai yiwuwa cikin kankanin lokaci.Hakan na nuna cewa, babu hali wata rana a ce an nada wani dan sarki a matsayin hakimi a masarautar ta Zazzau.Bisa al’ada ma ana zaben sarki ne daga cikin hakimai matukar yana da kwarewa a kan hakan. Ba cinya ba kafar ba Kenan, shi kuma kudirin dokar ya ce nadin masu anguwanni da suke karkashin hakimai, shi kuma yana nan a kan tsarin gado ne-babban shirme Kenan.


Yin katsalandan a cikin tsarin mulkin gargajiya,zai kawo karshen irin alakar da ke tsakani masarauta da kuma al’umarta. Za a nema martabawa a rasa. Duk wani sarki da yake mutunta tsarin mulkin sarauta ba zai goyi bayan wannan kudirin dokar ba ko da kuwa abin zai jawo masa matsala.


Akwai kwarin gwiwar cewa, gidajen sarauta na kasar Zazzau, za su hada kai wajen kin amincewa da wannan kudirin dokar da zarar majalisar dokokin jaha ta amince da shi.Kotu za ta umarci ElRufa’i da kada ya sanya wa kudirin dokar hannu. Akwai yiwuwar zai taka doka kuma ya sanya hannun don ganin kudirin dokar ya tabbata, amma hakan zai zama babban matsala domin da zarar ya bar mulki kotu za ta hukunta shi.


Dr Nasir Aminu - Cardiff



Recent Posts

See All

Comments


bottom of page