top of page
Dr Nasir Aminu

Tsaro: Yadda Gwamna El-Rufai Ke Aiwatar Da Bangaren

Harkar tsaro a jihar Kaduna yana da matukar muhimmaci kasancewar jihar cibiya ce a kasa ba ki daya. Sace daliban makarantar Sakandare ta Kankara, izina ce ga gwamnonin jihohi wanda hakkinsu ne su kare rayukan dukkanin mutanen da suke zaune a jihohinsu.


A lokacin da ake tambayar Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna a wani gidan talabijin game da sha'anin tsaro a jihar sai ya soma kauce-kauce da kawo hanyoyin gyara a maimakon ya dauki alhakin matsalar. Wanda yake fadin cewa ba alhakin gwamnoni ba ne wannan domin ba su suke da jami'an tsaro ba. Ko da yake Gwamnan jihar Zamfara ya ki yarda da shi, da ma wasu gwamnonin Arewa.


Gwamnatin tarayya tana daukan alhakin abubuwan da suke faruwa da dama. Amma El-Rufai ya ki yarda ya dauki alhakin hakan, duk da kudade da kayayyakin aikin da ake ba sa daga gwamnatin tarayya don magance matsalar tsaro. Kuma ma a tsarin Dimokradiyya babu wanda yake da ikon juya arzikin da kasa ke da shi, shi kadai..


Amma El-Rufai ya nunawa duniya cewa matsalar tsaro a jihar ba laifinsa ba ne. Amma zai iya tunawa a kwanakin baya ya umurci 'yan sanda su bi gida-gida su kwato kayayyakin tallafi da masu zanga-zanga suka yi wasoso. Wannan ya nuna cewa harkar tsaro ba daga Abuja and bayar da umurni ba.


A shekarar 2016 lokacin da lamura ke tafiya daidai, El-Rufai ya bugi kirjin cewa ya tura jami'an tsaro a yammacin Afrika su daidaita rikicin makiyaya. An nuna faifan bidiyo na El-Rufai da jami'an tsaro suna shiga cikin daji don neman 'yan bindiga a hanyar Abuja zuwa Kaduna.


Idan muka koma baya kadan a 2015 El-Rufai ba ya korafin haka sai kwanan nan. A 2018 daya daga cikin masu taimaka wa El-Rufai ya kalubalanci Gwamna Ortom na jihar Benue kan cewa da ya yi Gwamnatin tarayya ta gaza wajen Samar da tsaro a jiharsa. Amma da El-Rufai ya yi kwatankwacin haka, shiru ake ji.


A shekarar 2014 El-Rufai ya soki Gwamna Ramalan Yero kan cewa ya karbi kudi na tsaro daga gwamnatin tarayya Naira bilyan 4.8 amma babu abun da ya yi da su.


Amma da Shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya kalubalanci Gwamna El-Rufai kan yadda aka kashe kudaden tsaro da Gwamantin tarayya ta bai wa jihar a 2017, sai Gwamnan ya bayyana hanyoyi 4 da suka kashe kudaden.


Da farko ya ce sun kashe Naira bilyan 2.6 wajen taimakawa jami'an tsaro na Gwamnatin tarayya a bangaren sadarwa da jin dadin su.


Na biyu kuma ya ce sun kashe Naira bilyan 1.5 wajen Samar da CCTV camera a cikin Gari.


Na uku kuma sun kashe Naira milyan 193 wajen bibiyan layukan inda masu garkuwa da mutane ke buya.


Na karshe kuma sun yi amfani da Naira milyan 265 wajen amfani da na'urar daukan bidiyo (drone) wajen bibiyan 'yan ta'adda.


Dukkanin wadannan abubuwa a takarda fa suke domin babu su a fili. A takaice ma ba su amfanar da mutanen Kaduna ba, wajen kare rayukansu.


A watan Agusta 2020, Gwamna El-Rufai ya ce sun kashe Naira bilyan 16 a cikin shekaru 5 a bangaren tsaro, ya faÉ—i haka ne a taron majalisar tsaro na Sarakuna a jihar, abun mamaki babu wanda ya tambaya a cikinsu me aka yi da su kuma ta yaya.


A watan da ta gabata wani dan majalisar dokokin jihar ya nemi taimako daga tawagar shugaban kasa karkashin jagorancin Shugaban ma'aikatan fadar Shugaban kan sha'anin tsaro, a maimakon a yi bincike a maganar da ya yi a dauki mataki, hakan bai yiwu ba, sai dai abun da ya fada ya rika yawo a kafafen yada labarai na zamani.


Daga karshe ya kamata Gwamantin jihar Kaduna ta bi matakan da majalisar wakilai suka dauka na bincikar kudaden da aka kashe kan tsaro.


Idan haka ta faru za a sami cikakken tsaro kuma zababbun shugabannin za su rika daukan nauyin abubuwan da suke wuyansu, domin daukan nauyin abubuwan da suke wuyan shugabannin shi ne alamun shugabanci na gari.


Daga Nasiru Aminu

24 views0 comments

Комментарии


bottom of page